BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da shida
Ina matsayin auren kashe wuta da wasu kan yi don su koma gidan mijinsu na da?
TAMBAYA: Akramakallahu.'Yan uwa suna kira na Musa Waki'a; ko ya halatta na rika amsawa? Idan bai halatta ba, me ya kamata na yi kenan?
Daga Musa Muhammad Lafiya 080569670
SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani dai, suna mai kyau ya kamata mutum ya amsa. Kuma mafi kyau shi ne mutum a kira shi da sunan mahaifinsa, shi ne ya fi alhairi. Amma ba laifi da jingina mutum da wani abin da ake iya gane shi. Ko garinsu ko kabilarsu, ko gidansu, ko sana'arsa, ko wani abu mai kama da haka nan.
TAMBAYA: Akramakallah. Idan mutun yana da filaye da yawa, idan shekara ta yi zai iya fitar masu da zakka kenan?
Daga Muhammad Sani daga Kaduna Road a Suleja jihar Neja 0803 634 9052
SHAIKH ZAKZAKY: A'a lallai ba a zakkan fili. Abubuwan da ake ma zakka sanannu ne, kuma daga cikinsu lallai ba a fid da ma gona a matsayin gona kanta, sai dai gallar gona din ne ake ma zakka. Saboda haka sai dai in ya yi noma a filin nasa ya kai mikidarin zakka, ya fitar. Kuma idan filin (tun da fili ya ce), idan fuloti ne ya saya don gina gida, to har in bai gina gidan ba, a fatawar wasu Malamai, kamar Ayatullah Sistani, yana ganin cewa Khumusi zai hau kansa. Amma a fatawar Sayyid Khamne'i, yana ganin in dai shi mabukaci ne ga gidan, kuma sai ya bi mataki-matakai kafin ya gina gidan, ya sai fuloti awwalan, sannan kuma ya sai bulo, saniyan, sannan ya yi kaza, salisan, hawan-hawawa, to matukar yana yin gini, ba zai ba da khumusi ba har sai ya kammala. Da sharadin shi mabukaci ne ga gidan kenan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam idan mutum ya saki matarsa saki uku, sai suka shirya da wani ya aure ta don ya sake ta ya sake aura, yin hakan yana halatta?
Daga Muhammad Sani daga Kaduna Road a Suleja jihar Neja 0803 634 9052
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ba ya halatta, ba a yin kwangilar aure. Abin da aka sani kawai ita dai ta yi aure ne da sunan aure kuma suka rabu. Har ma idan aka fahimci da wannan shiri din na shi ya aura ne don ya saka, in an san dama da Deal (yarjejeniya) ne suka yi, to ana iya ma hana auren. Saboda ana yin aure ne tsakani da Allah. Ka ga ita matar an yaudare ta kenan. An nuna mata an aure ta ne alhali kuma ba aurenta aka yi ba, an biya wani mutum ne kawai ya take ta don ta zama halas ga wani. Kuma ba za ta ma zama masa halas din ba, saboda wannan ba aure bane yaudara ne. Kodayake shi bai bayyana ya yi yaudaran ba. Saboda haka kamata ya yi dai ya zama ta yi aure ne mai sunan aure ba yaudara aka yi ba. Kuma da fatan shi ma yi fahimci ma'anar saki uku din. Don galiba irin wannan mishkilan yakan faru ne a irin wadanda suka yarda da saki uku a kalma guda. Amma idan sakin sunna ce, yana da wuyar gaske irin wannan ya auku.
TAMBAYA: Wani lokaci kuma ai da matan ne akan hada baki a shirya auren kashe wuta?
SHAIKH ZAKZAKY: To ala ayyi halin, ko haka nan din ne, mu dai abin da muka dai sani kenan cewa ba a yin yarjejeniyar aure don a rabu. Akwai Duruf din aure, an yarda a yi aure Munkadi'i, sunansa ne dama, Munkadi'i, wanda wasu ke haramtawa, amma ba mu san wani abin da ya haramta shi ba a sunnar Annabi. To shi sunansa munkadi'i. Amma ba a yin aure da yaudara. Wani ya san cewa ya yi ne. Kamar ita ta yi ne da nufin za ta rabu da shi, ko kuma shi ya aure ta (amma bai gaya mata ba) yana nufin zai rabu da ita. Har in an gano haka nan, to an san yaudara kenan ba aure ba.
TAMBAYA: Akramakallah. Ni dan kasuwa ne ina sai dai riga, sai wani ya zo ya ce nawa ne saboda Allah? Sai na gaya masa kudin. Sai bayan ya tafi na tuna na yi masa kari, ya zan yi?
Daga Muhammad U/Azara Gwagwalada Abuja 0803 636 7110
SHAIKH ZAKZAKY: Idan dai ka gaya masa tsakani da Allah, zai zama ka gaya masa irin yadda kake siyarwa ne, duk da kuma ribar da kake ci wanda aka saba. Saboda haka ba lalle ne ya zama nawa kai ka sayo ba. In dai rigar sannanen abu ne tana da farashi sananne wanda kowa ya san farashinta ba ya wuce haka nan, to lallai irin wannan ne za ka gaya masa. Har kuma in ka gaya masa ba haka ba, in ya saya sai ka je ka mayar masa da ragowar abin da ka kara masa, ka ce ka yi masa karya ya yafe maka. Kuma ka roki Allah gafara saboda an tambaye ka ka fadi gaskiya tsakani da shi (Allah ), ka yi karya. Saboda haka wannan yana cikin nau'in yaudara a ciniki, abin da ka karan ba zai halatta maka ba.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Wasu suna cewa mu da muke karatun allo, wai haramun muke yi. Malam ya abin yake ne?
Daga Muhammad Nura Taura 0803 971 1079
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai babu inda aka ruwaito haramcin karatun allo. Yin karatun allo wata dabara ce ta yin karatu cikin sauki. Amma ba a ce lallai ne a yi ba, ana iya yi a takarda ko a bango, ko a kyalle, ko ma a yaya ne. Amma na allo wata dabara ce sassauka na yin karatu din. Amma a ce haramun ne lallai wannan ba haka bane.
TAMBAYA: Akramakallah. Da zuwa makaranta, da yi wa iyaye hidima, wanne ne ya fi muhimmanci?
Daga Abdullahi Abdullahi Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: To duk ne za ka yi daidai gwargwadon hali, daya ba ya hana daya. A cikin ayyukan da sukan zama wajibai da wadanda sukan zama ihsani, ba a kan kwatanta wani da wani ba. Sai dai a yi daidai gwargwadon kowanne yadda ba zai cutar da daya ba, lasiman karatu din, bai kamata ya yi hidimar iyaye ya cutar da karatu ba, amma kuma ba wai ba za a yi hidimar bane.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum zai iya amfani da kirgen wata daga rediyon Iran, musamman a kan abin da ya shafi azumi da sallar layya?
Daga Abdullahi Abdullahi Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: A'a lalle ba zai yiwu ba, saboda akwai bambancin sashi tsakanin nan da Iran. Saboda haka yana iya yiwuwa lissafinmu ya bambamta da kwana daya, wani lokaci ma har biyu. Saboda haka za a yi la'akari da ganin wata a inda kake ne, su kuma can da yake tsakaninmu da tazara mai nisa har ufuk dinmu ya bambamta, to kwanan watanmu na iya bambamta. Kodayake yana iya zuwa daidai kuma.
TAMBAYA: Gafarta Malam. Idan mutum ya zo yin waya yana yin minti daya da misalin dakika biyu, menene hukuncin dakikokin da ke saura a wajen masu yin wayar GSM ta haya, da yake mun lika cewa minti daya ne Naira 20? Zan iya yin amfani da wanann sauran dakikan da wannan mutumin ya bari?
Daga Ahmad Sa'aid Ahmad Hizbullah Chemist Potiskum jihar Yobe
SHAIKH ZAKZAKY: To ya danganta da yadda ainihin yarjejeniyar take ne. Idan kammalallun mintuna ne ake biya, ka ga ba ruwansu da abin da ya yi kasaru, wato ko ma bayan daya ko abin da ya fi daya kenan. Saboda haka wanda ya bar raguwar kasa da minti, shi ba mabukaci ne ga shi ba. Shi kuma wanda ya shigar, in ya kammala, shi kuma mintunansa ne kammalallu za a ce ya biya. Sai dai idan akwai wani tsari da ya nuna ana biyan har sakan (dakika) ne, wannan kuwa. Ya danganta da yadda tsare-tsaren suke; idan suna bin minti-minti ne babu ruwansu da abin da ya karu ko ya yi saura, saboda haka wani na iya samun 'bonus' wani na iya barin 'bonus' kenan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam don Allah ya ake yin zumunta, kuma menene ya zama wajibi a hakkin zumunta? Yaya mutum zai yi da 'yar uwarsa ajanibarsa wajen sauke hakkin zumunta, musamman idan aka yi la'akari da halin talauci da jama'ar kasar nan suke ciki?
0802 727 4921
SHAIKH ZAKZAKY:Abin da muka sani shi ne hakkin zumunci yana nufin ihsani ne daidai gwargwado da kuma ziyara ta gaisuwa. Kuma mutum yana yi daidai gwargwadon hali ne, ba a kallafa masa abin da ba ya iyawa ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ya batun da wasu suke yi na cewa idan mutum ya mutu an kulle fayil dinsa na alheri da kuma na sharri. Amma kuma na ji wasu Malaman sun ce akwai wasu ayyuka da mutum zai yi kafin ya mutu ladansu ya rika saduwa da shi. Wai ya abin yake ne?
Daga Nura Mu'azu Kano 0802 469 6903
SHAIKH ZAKZAKY: To shi wanda ya mutu kam, lallai ba wani aikin da shi a kashin kansa zai yi ya sami lada. Alal misali ba zai yi sallah ba. Ba zai yi azumi ba, ba zai yi istigfari ba, ba zai yi duk ayyukan ibada ba, tunda ya mutu. Abin da masu cewa in ya mutu an kulle fayil dinsa suke nufi kenan. To amma (ayyuka) wanda dama ya yi yana da rai, wanda amfaninsa yana nan ya wanzu, to zai samu amfaninsa ko bayan ya mutu. Ka ga wato aikin in ka lura ai ba daga kabari ne yake yiwo ayyukan ba, ya riga ya yi ne kafin ya tafi kabarin. Kamar ilimin da ya bari ana amfana da shi, ko kuma gini da ya gina kamar na masallaci ko na makaranta ana amfani da shi, ko kuma ya bar mutane suna ta yi masa addu'o'i. To ka ga duk wannan zai amfane shi. Amma ka ga ba shi ne yake aikin ba ai, ya riga ya yi ne kafin ya mutu. Saboda haka wannan bai yi karo da wancan ba. Ba wai ana nufin in an kulle fayil din mutum ko da aikin alherin da ya bari sai ya ki bin sa bane. Kuma an ce ayyukan alheri suna bin shi bayan ya mutu, ba ana nufin shi ne yake ta yin su bayan ya mutun ba.